logo

HAUSA

Shugabannin kungiyoyin kasa da kasa da manyan jami’an gwamnati sun taya al’ummar kasar Sin murnar shiga sabuwar shekarar gargajiya

2023-01-22 16:20:50 CMG Hausa

Shugabannin kungiyoyin kasa da kasa, da manyan jami’an gwamnatocin kasashe daban-daban, sun isar da sakon gaisuwa zuwa ga daukacin al’ummar kasar Sin, da Sinawa dake zaune a fadin duniya, don taya su murnar shiga sabuwar shekarar gargajiya ta Zomo.

Cikin sakonta, shugabar asusun bada lamuni na duniya ko kuma IMF a takaice, Kristalina Georgieva, ta ce, “ina so in yi wa al’ummar kasar Sin, da ma’aikatan IMF ‘yan asalin kasar Sin, barka da sabuwar shekara, ina kuma yi musu fatan alheri tare da abokai da ‘yan uwansu, da fatan kasancewa cikin koshin lafiya, da jin dadin rayuwa a shekarar Zomo.” Kristalina Georgieva ta kuma yi wa kasa da kasa fatan kara samun ci gaba cikin hadin-gwiwa a sabuwar shekarar.

Ita ma a nata bangaren, babbar darektar kungiyar kasuwanci ta duniya wato WTO, Ngozi Okonjo-Iweala, ta taya kasar Sin gami da al’ummar ta murnar shiga shekarar Zomo, tana mai fatan Allah ya maimaita.

Shi ma a nasa bangare, shugaban kasar Zimbabwe, Emmerson Mnangagwa, ya mika gaisuwar murnar shiga sabuwar shekara ga jama’ar kasar Sin, da fatan Allah ya ba su koshin lafiya, ci gaba da nasara a shekarar Zomo. (Murtala Zhang)