logo

HAUSA

Matsalar shaye-shayen miyagun kwayoyi na ta azaara daga wajen matasa a Nijar

2023-01-22 17:10:56 CMG Hausa

Matsalar shan miyagun kwayoyi daga wajen matasa na daya daga cikin manyan matsalolin dake daukar hankalin shugabannin kasar Nijar dama kuma uwayen yara. A yau babu wani yankin Nijar da ba ya fama da shaye-shaye miyagun kwayoyi da makamantasu, kuma yawanci matasa ne mata da samari suke rungumar wadannan kayan maye. Ganin yadda wannan matsala take kamari ne ya sa mutane suka fara kiraye-kiraye da a dauki matakai domin magance wannan matsala tun da sauran lokaci. Daga birnin Yamai, wakilinmu Mamane Ada ya hada mana wannan rahoto.

Matsalar shan miyagun kwayoyi  wajen matasa na daya daga cikin manyan matsalolin dake daukar hankalin shugabannin kasar Nijar. Dalilin kafa wata hukumar musamman da aka dora ma nauyin yaki da fataucin miyagun kwayoyi da makamantansu, cewa da OCRTIS, inda a ma kwanan nan hukumar ta kama birgin tabar wiwi guda 335 a nan birnin Yamai. A cewar hukumar, wannan kamu ba irinsa ba ne na farko a Yamai har ma a wasu yankuna kamar Maradi, Tahoua, Zinder da Agadez. A cewar masanin zamantewar dan adam, dole sai an tashi ka-in-da-na-in domin ciwo kan wannan matsala, in ji Issa Alou Aye.

"E gaskiya babbar matsala ce wadda muke nan muna tunkara a rayuwarmu ta yanzu, ita ce ta shaye shaye. Idan an tsaya an yi nazari ana cewa shaye-shaye ya jima cikin duniya. Amma yau a wayi gari a kwana a tashi, ya zama ruwan dare game duniya. Yau da wuya za ka iske gungun samari, gungun ’yan mata wadanda ba a samu suna shaye-shayen nan."

Sai dai kuma wasu matasan dake kokarin tafiyar da sana’o’insu, kamar Murtala mai sana’ar saida shayi da burodi na ganin dole matasa su yi wa kansu wa’azi.

"Matasa saura masu shaye-shaye, E zan iya daukar sauran rashin sanin ciwon kai, saura kuma rashin kulawa daga bangaren iyayensu."

Shi kuma malam Issaka L’Homme, na ganin cewa, matsalar shaye shayen miyagun kwayoyi, babbar matsala ce ga makomar matasa, iyaye suna da nasu laifin kan wannan matsala.

"E to zargin da ake mana mu uwaye ina ganin daidai ne ma a zarge mu tun da idan wani ya fake dansa ya yi ma dansa magana, dan ya ji, wani uba ko da ya yi wa dansa magana ba ya ji ba, ba zai saurare shi ba. To ka gani nan ma akwai matsala. Da uba da uwa su dage zuwa makarantar yara, domin inda babu ilimi, babu makaranta to tashin hankali ya zo a cikin gida ma, kuma barna ta zo a cikin kasa gaba daya, ba mu son haka nan, muna son yaranmu su rika zuwa makaranta, su samu ilimi, ilimi shi zai kori jahilci kuma ilimi shi zai kore shaye-shaye."

Shin mene ne ke tura ’yan matasa da samari sun sha miyagun kwayoyi da makamanta nasu, kuma wadannan illoli ne ga kasa da kuma al’umma, tambayoyin da sake aza ma Issa Alou Aye, masanin zamantekewar dan Adam, ga kuma abin da yake cewa,

"Ya zama ragaggen mutum a wajen mu amalarshi tare da ’yan uwanshi a kuma wajen lafiyar jikinsa ma. Dan saboda a kulluyomin ba ka iyar rayuwa saida su, wadannan kayan mayen nan ai an yi asarar mutum. Akwai sakacin da aka yi ya sa yau kwayan nan  ta zama ga ta nan ko ina, a hannun yara kanana, a hannun manya, a hannun lattizawa, ka ga shaye-shaye, ka ga kashe-kashe, ka ga sace-sace da suka yi yawa ko nan Yamai, to dukka wannan yana cikin illa domin duk wanda yana cikin maye hankalinsa babu, wanda bai da hankali kome aka ce ya yi to kada ka yi gardama."

Kamar da yadda malam Bahaushe ke cewa karfe tun da zafinsa ake iyar lankwasa shi, ke nan ya rataya kan hukumomin kasa da suka kara daukar matakai domin kare wadannan matasa. (Mamane Ada)