logo

HAUSA

An yi murnar shiga sabuwar shekarar Zomo ta kasar Sin a fadin duniya

2023-01-22 17:12:51 CMG Hausa

Daga kasashen Thailand da Serbia, zuwa New Zealand da Amurka da ma kasashen Afirka, an yi ta murnar shiga sabuwar shekarar gargajiya ta kasar Sin wanda ya fado a yau, 22 ga watan Junairun.

An gudanar da tarukan liyafa, kana an kunna jajayen fitilu a muhimman gine-gine. Baya ga haka, an gudanar da wasanni kamar na raye-rayen dabbobin Dragon da Zaki. Kana a sassan daban-daban dake fadin duniya, ana iya ganin jajayen fitilun gargajiya na Sinawa da sauran kayayyakin ado masu dauke da siffofin Zomo, wadda ita ce dabbar dake wakiltar sabuwar shekarar 2023 ta gargajiya ta kasar Sin.

A karon farko a Jamhuriyar Afrika ta Tsakiya, shugaban kasar Faustin-Archange Touadera, ya shirya wani katafaren liyafar murnar shiga sabuwar shekarar gargajiya ta kasar Sin a fadar shugaban kasa, wanda ya samu mahalarta sama da 300. Shugaba Toadera, ya yi fatan samun sabon ci gaba a dangantakar kasashen biyu a sabuwar shekarar.

A Kenya kuwa, cibiyar Confuscius dake jami’ar Nairobi, ta gudanar da wani taro na murnar sabuwar shekarar gargajiya ta Sin.

Su kuwa al’ummar Sinawa mazauna Ghana, sun yi maraba da sabuwar shekarar ce ta hanyar shirya wata kayatacciyar liyafa a daren Juma’a, inda aka gabatar da fasahohi da al’adun gargajiya na kasar Sin, ciki har da salon raye-raye daban-daban, wanda ya sanya Sinawan da suka yi nesa daga gida cikin yanayi murnar bikin tamkar a gida.