logo

HAUSA

Botswana ba za ta yi wa matafiya daga kasar Sin gwajin cutar COVID-19 ba

2023-01-21 16:05:36 CMG Hausa

Ma’aikatar kula da lafiya ta kasar Botswana, ta ce kasar ba za ta kakaba dokoki ga matafiya daga kasar Sin, kamar yadda wasu kasashen yammacin duniya suka yi ba.

Ministan lafiya na kasar Edwin Dikoloti ne ya bayyana haka ranar Alhamis yayin da yake zantawa ta wakilin kamfanin dillancin labarai na Xinhua ta wayar tarho, inda ya ce Botswana ta aminta da dabarun kasar Sin na dakile duk wata cuta mai saurin yaduwa, musammam COVID-19, bisa la’akari da nasarar da ta samu bayan barkewar cutar. Don haka, babu bukatar shakku game da karfin kasar Sin na yaki da cututtuka masu yaduwa.

Ya kara da cewa, hakika, Botswana ta amfana sosai daga shawarwarin da Sin ta gabatar dangane da yaki da cutar COVID-19 a lokacin da cutar ta barke a kasar a watan Maris na 2020. Yana mai cewa, ba don kasar Sin ba, da Botswana ta yi asarar dimbin rayuka.

Bugu da kari, Ministan ya ce wajibi ne kasashen yammacin duniya su bari yaki da cutar ya kasance bisa kimiyya, saboda siyasantar da ita ba zai taimaka ba, mayar da hannu agogo baya kadai zai yi. (Fa’iza Mustapha)