logo

HAUSA

Shagalin murnar bikin bazara ya gabatar da shirye-shirye masu ban sha'awa ga Sinawa a duk duniya

2023-01-21 20:10:09 CMG Hausa

A yau Asabar jajibirin sabuwar shekarar gargajiya ta kasar Sin da karfe 8:00 na daren, aka soma nuna shagalin murnar shiga sabuwar shekarar gargajiya ta kasar Sin da babban rukunin gidan rediyo da talabijin na kasar wato CMG ya gabatar ga Sinawa dake wurare daban daban na duniya.

Kundin abubuwan da suka yi fice a duniya na Guinness World Records ya amince da wannan shirin talabijin a matsayin "Shagalin talabijin da aka fi kallo a duniya", tun daga shekarar 1983, wanda akan gabatar da shi a kowanne jajibirin sabuwar shekarar gargajiya ta kasar Sin kamar yadda aka tsara har tsawon shekaru 40.

A shekarar 1983 ne, gidan talabijin na kasar Sin wato CCTV, ya watsa shagalin murnar shiga sabuwar shekara na farko na bikin bazara kai tsaye. Tun daga wancan lokacin, kallon "Shagalin murnar bikin bazara" tare da daukacin iyali a jajibirin sabuwar shekara ya zama wata muhimmiyar al'adar sabuwar shekarar gargajiyar Sinawa, kamar yin dumplings da manna takaradun fatan alheri na bikin bazara. Shirye-shiryen masu ban sha'awa da aka gabatar a cikin "Shagalin murnar bikin bazara" na tsawon shekaru, sun zama abin tunawa da bikin bazara ga daruruwan miliyoyin Sinawa.

Shagalin murnar bikin bazara na shekarar 2023 yana manne da manufar dake hade da tunani da fasaha, da koyi daga kyawawan al'adun gargajiya na kasar Sin, da rayuwa ta hakika, da kuma hazakar wayewar kasashe daban-daban na duniya, tare da fasahohin zamani da fasahar haske da inuwa, don nuna shirye-shiryen kade-kade da raye-raye, da wasannin kwaikwayo masu ban dariya, da wasannin gargajiya, da wasan Kungfu da sauransu. Abin lura shi ne, sakamakon sabbin fasahohi masu yawa da aka yi amfani da su, shagalin na bana ya samu sabbin ci gaba a fannin tasirin sauti da hoto.

A ranar 21 ga wata, a jajibirin sabuwar shekarar gargajiya ta kasar Sin, shagalin murnar bikin bazara na shekarar 2023 ya bi Sinawa dake duk fadin duniya don bayyana fatansu a sabuwar shekarar zomo, tare da maraba da sabuwar shekara mai kyakkyawar makoma. (Mai fassara: Bilkisu Xin)