logo

HAUSA

Jami'an tsaron Kenya sun kashe mayakan al-Shabab 10

2023-01-19 12:35:41 CMG Hausa

Rahotanni daga kasar Kenya na cewa, jami'an tsaron kasar sun kashe 'yan ta'addar Al-Shabab 10, a gundumar Garissa da ke yankin arewa maso gabashin kasar.

Kwamandan ’yan sandan yankin arewa maso gabashin kasar George Seda ya ce, tawagar jami’an tsaro da dama ne suka gudanar da wani samame, kan maboyar kungiyar dake Degbon, bayan sun bi sawun ’yan ta’addan na tsawon mako guda.

Ya ce, kashe ’yan ta’addan, ya biyo bayan wani bayanin sirri da suka samu daga mazauna yankin. Yana mai cewa, ana ci gaba da gudanar da aikin, amma bai yi karin bayani ba.

Matakin na zuwa ne, kwanaki bayan da kungiyar ta'addancin ta kai wasu hare-hare a yankin, inda suka kashe mutane fiye da 10. Bugu da kari, ana zargin maharan da kashe wasu injiniyoyi hudu da ke aiki da hukumar kula da manyan tituna ta Kenya.

’Yan ta'addan Al-Shabab dai sun sha kai hare-hare a wurare a yankin, musamman a yankunan Mandera, da Wajeer, da Garissa dake arewa maso gabashin Kenya, bayan da suka kutsa kai cikin yankunan tsaro, lamarin da ya yi sanadiyar jikkata da mutuwar fararen hula da jami'an tsaro da dama. (Ibrahim Yaya)