logo

HAUSA

Dandalin TikTok ya karrama mafiya kwarewa wajen samar da bidiyo masu kayatarwa

2023-01-17 11:22:08 CMG Hausa

Dandalin dora gajerun bidiyo na TikTok, mallakin kamfanin ByteDance na kasar Sin, ya mika lambobin karramawa ga masu amfani da dandalin mafiya kwarewa, wajen samar da bidiyo masu kayatarwa, daga sassan nahiyar Afirka daban daban.

An gudanar da bikin karrama taurarin TikTok din ne a karshen makon jiya a birnin Nairobin kasar Kenya, da nufin jinjinawa gudumawar ’yan TikTok mafiya hazaka, bisa gudummawarsu ga ci gaban dandalin cikin shekarar da ta gabata.

An dai fafata har tsawon kwanaki 8, a gasar nuna bajimtar bayar da labarai, da nuna basirar kirkire-kirkire, da zuwa da sabbin abubuwa, da samar da abubuwa masu kyakkyawan tasiri ga al’umma, a kan dandalin na TikTok, kafin kaiwa ga zabar gwarazan gasar daga kudanci, da yammaci, da gabashin Afirka.

Bayan tantance ’yan takarar, a cewar jagorar sashen lura da abubuwan da ake dorawa kan dandalin a shiyyar kudu da hamadar Sahara Boniswa Sidwaba, a shekarar 2022, dan takara Dennis Ombachi wanda aka fi sani da @theroamingchef daga kasar Kenya ne ya zamo zakaran gasar, sai na biyu, Charity Ekezie, wanda aka fi sani da @charityekezie daga Najeriya.

Sidwaba ta kara da cewa, zakaran gasar daga yammacin Afirka shi ne @e4ma daga Najeriya, sai na shiyyar kudancin Afirka wato @Pilot_onthegram dan kasar Afirka ta kudu, yayin da @natasha_gwal daga Kenya ta zamo zakara a gabashin Afirka. (Saminu Alhassan)