Shugaba Xi Jinping ya mika sakon ta’aziyya ga takwarar aikinsa ta Nepal game da hadarin jirgin sama a kasar
2023-01-17 20:37:35 CMG Hausa
Shugaban kasar Sin Xi Jinping ya mika sakon ta’aziyya ga takwarar aikinsa ta kasar Nepal Bidhya Devi Bhandari game da hadarin jirgin saman fasinja da ya faru a kasar.
Shugaba Xi ya bayyana cewa, ya san hadarin jirgin saman fasinja da ya faru a kasar Nepal, wanda ya haddasa mutuwar mutane da dama. Kuma a madadin gwamnatin kasar Sin da jama’arta, yana ta’aziyya da jaje ga iyalan mutanen da suka mutu sakamakon hadarin. (Zainab)