logo

HAUSA

Shugaban Masar Abdel Fattah Al-Sisi ya gana da Qin Gang

2023-01-16 11:23:12 CMG Hausa

Shugaban Masar Abdel Fattah Al-Sisi, ya gana da ministan wajen Sin Qin Gang, wanda ke ziyara a birnin Alkahira a jiya Lahadi 15 ga wata.

Yayin zantawarsu, shugaba Al-Sisi ya bayyana cewa, Sin babbar kasa ce, wadda ba za a iya hana ta ci gaba ba, kuma ba za a iya lalata dangantakar abokantaka dake kasancewa tsakanin Masar da Sin ba. Kaza lika Masar za ta ci gaba da tsayawa tsayin daka kan manufar kasar Sin daya tak a duniya, da nuna adawa ga kasashen waje masu tsoma baki cikin harkokin siyasa na cikin gidan kasar Sin.

Shugaba Al-Sisi ya kara da cewa a kwanakin baya, bangaren Sin ya kyautata manufofin kandagarki da kawar da cutar COVID-19, kuma jama’ar Masar na maraba da zuwan abokansu na Sin, cikin kasar domin yawon shakatawa ba tare da bata lokaci ba.

A nasa bangare kuwa, Qin Gang ya bayyana cewa, bangaren Sin yana goyon bayan Masar, wajen bin hanyar ci gaba da ta dace da yanayin kasar, da kare ikon mulkin kasa, da tsaron kasa, da kuma cin gajiyar bunkasar kasa. Ya ce ana fatan za a inganta ayyukan hadin gwiwa masu muhimmanci tsakanin bangarorin biyu, da kuma samun sakamako a Masar a fannonin bunkasa manufar “Ziri daya da hanya daya” a taron kolin Sin da Saudiyya.

Qin Gang ya ce, bangaren Sin ya yaba, da kuma tsayawa tsayin daka kan matsayar Masar ta taka rawar gani kan inganta zaman lafiya da kwanciyar hankali na Gabas ta Tsakiya, ana kuma fatan Sin da Masar za su inganta zaman lafiya da tsaron yankuna tare, da kuma inganta warware batun Falasdinu cikin sauri da adalci.

Bayan ganawar, Qin Gang ya kuma gana da takwaransa na Masar Sameh Shoukry. (Safiyah Ma)