logo

HAUSA

Hadarin babbar mota a Nijeriya ya haddasa mutuwar mutane 16 da jikkatar mutane 83

2023-01-16 12:53:33 CMG Hausa

Bisa sanarwar da hukumar kula da hanyoyi ta jihar Filato dake tsakiyar Nijeriya ta bayar a jiya Lahadi, an ce, wani hadarin babbar mota da ya faru a ranar Asabar 14 ga watan nan, ya haddasa mutuwar mutane 16, da kuma jikkatar mutane 83.

Hukumar kula da hanyoyi ta jihar Filato ta sanar da cewa, babbar mota dake dauke da fasinjoji fiye da kima, ta yi hadari ne saboda gudun waje sa’a, a daren Asabar a yankin Mangu na jihar.

Yayin da lamarin ya auku, motar na dauke da fasinjoji 99 da kuma direba, kuma cikin su fasinjoji 16 sun rasu, kana sauran 83 sun ji raunuka. An kuma garzaya da wadanda suka ji raunuka asibiti domin karbar jiyya.

Hukumar kula da hanyoyi ta jihar Filato, ta yi kira ga al’ummar jihar, da su kauracewa karya dokar hawan ababen hawa da karya ka'idar daukar fasinjoji. (Safiyah Ma)