logo

HAUSA

MDD: An kashe fararen hula 27 a gabashin DRC a wannan makon

2023-01-13 13:08:17 CMG HAUSA

 

Mai magana da yawun MDD Stephane Dujarric ya bayana cewa, ya zuwa yanzu, kungiyoyin da ke dauke da makamai a lardin Ituri na Jamhuriyar Dimokaradiyyar Kongo, sun kashe fararen hula a kalla 27 a cikin wannan mako.

A cewarsa, tawagar wanzar da zaman lafiya ta MDD a DRC, wadda aka fi sani da MONUSCO, ta bayar da rahoton cewa, halin da ake ciki a yankin Djugu ya yi kamari, bayan farmakin da mayakan gamayyar kungiyoyi masu dauke da makamai da aka fi sani da CODECO suka kai, inda suka kashe a kalla mutane 27 tun a karshen makon da ya gabata.

Ya kara da cewa, a yayin da MDD ke taimaka sojojin Congo, su ma dakarun wanzar da zaman lafiya na MDD suna gudanar da sintiri a yankin Roe-Drodo domin kare fararen hula. (Ibrahim Yaya)