Mataimakin firaministan Sin zai halarci taron shekara shekara na WEF a Switzerland
2023-01-13 20:00:09 CMG Hausa
Bisa gayyatar shugaban dandalin nazarin tattalin arziki na WEF Mr. Klaus Schwab, mataimakin firaministan kasar Sin Liu He, zai halarci taron shekara shekara na dandalin WEF na shekarar 2023 a Switzerland, tsakanin ranaikun 15 zuwa 19 ga watan nan na Janairu, kamar dai yadda kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar Sin Wang Wenbin ya bayyana a Juma’ar nan. (Saminu Alhassan)