logo

HAUSA

An kashe sojojin kasar Mali 14

2023-01-13 10:45:11 CMG Hausa

Ofishin hulda da jama’a da watsa labarai na rundunar sojojin kasar Mali ya sanar a cikin wata sanarwa cewa, an kashe sojojin kasar 14 a wani hari da aka kai yankin tsakiyar kasar ranar Talata.

Sanarwar ta bayyana cewa, an kai hare-haren bama-bamai kan dakarun tsaron Mali dake yankunan dake makwabtaka da garuruwan Dia da Diafarab, gami da na Koumara da Macina, duk a yankin tsakiyar kasar. Baya ga sojoji 14 da suka rasa rayuka, akwai kuma wasu mutane 11 da suka ji rauni, sakamakon hare-haren.

Daga bisani an tura karin sojoji zuwa wadannan wuraren, inda aka kashe ’yan ta’adda 31.

Sai dai babu wata kungiyar da ta sanar da daukar nauyin hare-haren da aka kaiwa sojojin har zuwa yanzu. (Bello Wang)