logo

HAUSA

Shugaban tarayyar Najeriya ya bukaci kasashen waje da kada su saka baki a babba zaben kasar dake tafe

2023-01-13 14:11:57 CMG HAUSA

 

A ranar Alhamis 12 ga wata sabbin jakadun kasashe 6 suka gabatar da takardun kama aikinsu ga shugaban tarayyar Najeriya Muhammadu Buhari a fadar gwamnati dake birnin Abuja.

Jakadun sun hada da na Switzerland, Sweden, Jamhuriyar Ireland da Thailand da Senegal da kuma Sudan ta Kudu.

Shugaba Muhammadu Buhari ya bukaci sabbin jakadun da su tsaya a iya aikin da hurumin doka ya tanadar masu na sanya ido a kan tsare-tsaren zabe da kuma sanya ido kan yadda zabukan za su gudana.

Ya ce bisa la’akari da kyakkyawar alakar dake tsakanin Najeriya da kasashensu, akwai bukatar su bayar da gudumawarsu wajen tabbatar da ganin Najeriya ta fita daga matsalolin da suke ci mata tuwo a kwarya, musamman ma batun tsaro, yaki da cin hanci, fadada hanyoyin bunkasar tattalin arziki da kuma samar da shugabanci na-gari.

Koda yake dai shugaban Buhari ya yaba mutuka da irin gudummawar da kasashen suke baiwa gwamnatinsa a yakin da take yi da kalubalen tsaro wadanda suka kunshi garkuwa da mutane da kuma ’yan ta’adda, masu safarar miyagun kwayoyi kana da kokarin dakile illar annobar muhalli wanda ya samo asali daga matsalar sauyin yanayi a yankin tafkin Chadi, inda ya ce babu kasar da za ta iya shawo kan wadannan matsaloli ita kadai.

Shugaba Muhammadu Buhari ya kuma ci gaba da cewa, “Babu wata tantama Najeriya tana jin dadin yadda alakar dake tsakaninmu da kasashenku ke kara igantuwa, wannan ya nuna a fili irin namijin kokarin da jakadun da suka gabace ku suka nuna kafin barinsu kasar nan. Ina son amfani da wannan dama wajen sanar da ku cewa bangarorin ilmi da kiwon lafiya da harkokin noma da bunkasar kananan masana’antu da harkokin sufuri da bunkasa bangaren ma’adanai su ne bangarorin da muke matukar bukatar tallafin masu saka jari daga ’yan kasashen waje.”

Da yake jawabin godiya a madadin sauran jakadun, jakadan kasar Switzerland Ambasador An-nika Hahn Eng-lund ya tabbatarwa shugaba Buhari cewa za su yi aikin su bisa nuna kwarewa tare da bin dokokin kasa da kasa ta yadda alakar dake tsakanin kasashen su da Najeriya za ta kara yaukaka.

Ya kuma cigaba dacewa..

“A madadin sauran takwarori na ina farin ciki gabatar da godiyar mu a gareka bisa yadda ka karbe mu yau din nan, babu shakka irin kwarywa-kwaryar bikin da sashen karbar baki ya shirya mana abin a baya ne mutuka”

Daga bisani yayi fatan Najeriya zata gudanar da harkokin babban zabe ta cikin kwanciyar hankali batare da cin karo da wani kalubale ba. (Garba Abdullahi Bagwai)