logo

HAUSA

Wani sabon nau’in Omicron na cutar COVID-19 na bazuwa cikin sauri a Amurka

2023-01-11 13:23:27 CMG Hausa

Cibiyar kandagarki da dakile yaduwar cututtuka ta Amurka, ta ce wani sabon nau’in Omicron na cutar COVID-19 na yaduwa cikin sauri a kasar, inda ta yi kiyasin kusan kaso 30 na wadanda suka kamu da cutar COVID-19 a karshen mako, sun kamu da sabon nau’in.

Bayanai na baya-bayan nan da cibiyar ta fitar, sun ce an yi hasashen sabon nau’in na XBB.1.5, zai kunshi sama da kaso 70 na kwayoyin cuta a wasu yankunan arewa maso yammacin kasar.

Nau’in na XBB.1.5, shi ne ya mamamye kaso 27.6 na jimilar wadanda suka kamu da cutar COVID-19 a karshen makon da ya gabata, inda ya tashi daga kaso 18.3 da ya kasance mako guda da ya gabata, da kuma kaso 11.5 a makonni biyu da suka gabata.

Haka kuma, sabon nau’in na yaduwa a wasu sassan Asia, lamarin da ke haifar da fargaba.

A cewar cibiyar ta CDC, wasu nau’ika biyu na Omicron wato BQ.1 da BQ.1.1, sun dauki kimanin kaso 55 na sabbin wadanda suka kamu da cutar a Amurka cikin makon da ya gabata. (Fa’iza Mustapha)