logo

HAUSA

Shugaban Gabon ya nada sabon firaminista

2023-01-10 10:37:57 CMG HAUSA

 

Shugaban kasar Gabon Ali Bongo Ondimba, a jiya Litinin ya nada Alain Claude Bilie By Nze a matsayin sabon firaminista kuma shugaban gwamnati.

Wata sanarwar shugaban kasar da babban sakataren fadar shugaban kasar Gabon Jean-Yves Teale ya karanta ta gidan talabijin na kasar, ta bayyana cewa, yanzu Bilie By Nze ne ke da alhakin kafa sabuwar gwamnati. Zai kuma maye gurbin Rose Christiane Ossouka Raponda, wadda aka nada a wannan rana a matsayin mataimakiyar shugabar kasar Gabon, mukamin da babu wanda ke rike da shi sama da shekaru uku.

Alain Claude Bilie By Nze, mai shekaru 56, ya rike mukamin mataimakin firaminista mai kula da makamashi da albarkatun ruwa. Yana aiki tare da Ali Bongo Ondimba, tun a watan Maris na 2012 lokacin da ya zama mai ba da shawara kan harkokin siyasa kuma kakakin fadar shugaban kasa. (Ibrahim Yaya)