logo

HAUSA

An rufe tashar jirgin kasa a Najeriya sakamakon harin 'yan bindiga

2023-01-09 10:36:40 CMG Hausa

Hukumomin jiragen kasa na Najeriya sun sanar da rufe tashar jirgin kasa a jihar Edo da ke kudancin kasar, har sai illa masha Allah, bayan wani hari da ’yan bindiga dauke da makamai suka kai a ranar Asabar din da ta gabata. 

Hukumar kula da zirga-zirgar jiragen kasa ta Najeriya (NRC) ta bayyana a cikin wata sanarwar da ta fitar cewa, daukar wannan matakin ya zama wajibi, sakamakon kalubalen tsaro da ake fuskanta. Hukumar ta ce, tana sanar da jama'a, musamman ma fasinjoji cewa, an rufe tashar na dan wani lokaci saboda matsalar tsaro, har sai an samu sanarwa daga gare ta. 

Rundunar ’yan sandan Najeriya ta shaida wa kamfanin dillancin labarai na Xinhua ta wayar tarho jiya Lahadi cewa, wasu gungun ’yan bindiga ne suka kutsa cikin tashar jirgin kasa ta Igueben da ke jihar Edo a ranar Asabar din da ta gabata, inda suka fara harbe-harbe a cikin iska, kafin su yi awon gaba da fasinjoji da dama da ke jiran a kai su garin Warri na jihar Delta. 

Sai dai rundunar ’yan sandan a cewar kakakinta, ta kaddamar da wani samame domin kamo ’yan bindigar da suka gudu tare da kubutar da wadanda aka sace. (Ibrahim Yaya)