logo

HAUSA

Shugaba Lula na Brazil ya lashi takobin hukunta wadanda suka kutsa cikin gine-ginen gwamnati

2023-01-09 11:18:47 CMG Hausa

 

Shugaban kasar Brazil, Luiz Inaciao Lula da Silva, ya yi tir da kutsen da magoya bayan tsohon shugaban kasar mai tsattsauran ra’ayi, Jair Bolsonaro suka yi cikin majalisar dokokin kasar da fadar shugaban kasa da kotun koli a jiya Lahadi.

Shugaba Lula ya bayyana a jiyan cewa, mutanen za su fuskanci fushin doka.

Ya kuma sanar da kasancewar dakarun tsaro na matakin kasa a Brasilia har zuwa ranar 31 ga wata, bayan tun da farko, masu zanga-zangar sun ci karfin jami’an tsaron birnin.

Kafafen watsa labarai a kasar sun ruwaito cewa, jami’an tsaro sun kwace iko da ginin majalisar dokokin daga hannun masu zanga-zanga, yayin da suke ci gaba da aiki a hedkwatar kotun koli da fadar shugaban kasa.(Fa’iza)