logo

HAUSA

Shugaban AU ya jajantawa al’ummar Senegal dangane da mummunan hadarin mota da ya auku a kasar

2023-01-09 11:30:04 CMG Hausa

Shugaban hukumar Tarayyar Afrika AU, Moussa Faki Mahamat, ya jajanta mummunan hadarin da ya auku a Senegal, wanda ya yi sanadin mutuwar mutane sama da 40.

Mutane 40 ne suka mutu yayin da wasu da dama suka ji rauni, bayan taho-mugamar da wasu motocin bas biyu suka yi, a yankin Kaffrine na tsakiyar kasar Senegal a jiya Lahadi.

Moussa Faki Mahamat ya wallafa a shafinsa na twitter cewa, yana ta’aziyya da jaje ga iyalan wadanda hatsarin ya rutsa da su, wanda ya yi sanadin mutuwar mutane sama da 40 a Senegal, kana ya yi wa wadanda suka jikkata fatan samun sauki cikin gaggawa, tare da bayyana goyon bayansa ga shugaban kasar Macky Sall da gwamnati da al’ummar Senegal.

Shugaban Senegal Macky Sall ya ayyana makokin kwanaki 3 a kasar, inda ya ce wani kwamitin da ya kunshi ma’aikatu daban daban zai tattauna a jiyan, domin daukar matakai masu kwari na tabbatar da kiyaye haddura tituna da kare lafiyar fasinjoji. (Fa’iza Mustapha)