logo

HAUSA

Najeriya za ta fara samar da kayayyakin gwaje-gwajen kimiya ga manyan makarantun kasashen Uganda da Kamaru da kuma Kodibuwa

2023-01-07 14:25:28 CMG Hausa

A ranar 6 ga wata ne mataimakin shugaban hukumar inganta fasahar kere-kere ta tarayyar Najeriya NASENI Farfessa Mohammad Haruna, ya sanar cewa kasashen Afrika 3 Uganda da Kamaru da kuma Kodibuwa sun mika bukatarsu ga hukumar wajen samar da kayayyakin gwaje-gwajen kimiya ga manyan makarantu da kuma makarantun sakandaren kasashen.

Ya tabbatar da hakan ne yayin fira da manema labarai a birnin Abuja bayan wata ganawar sirri da ya yi da shugaban kasa Muhammadu Buhari a fadar gwamnati.

Ya ce a ranar Alhamis 5 ga wata hukumar tasa ta karbi takardar bukatun wadannan kasashe, tare da kulla yarjejeniyar biyan kudin kai tsaye ga asusun gwamnatin tarayyar Najeriya.

Farfessa Muhammadu Haruna ya ci gaba da cewa yanzu haka hukumar ta fara zama daya daga cikin hukumomin da suke tarawa gwamnati kudi kamar sauran hukumomi ta hanyar kirkire-kirkiren fasaha da hukumar ke yi.

Ya ce baya ga samar da kayayyakin gwaje-gwajen kimiya, hukumar tana da masana`antar samar da hasken wuta ta amfani da rana wanda yana daya daga cikin kamfanonin gwamnati da ake da masu hannun jari a ciki.

Mataimakin shugaban hukumar ta NASENI a tarayyar Najeriya ya kuma tabbatar da cewa a zango na biyu na wannan shekara, gwamnati za ta biya kamfanin kere-keren fasaha na kasar Sin wato China Great Wall Corporation ragowar kaso 15 na adadin kudi dala miliyan 325.86 domin samar da kamfanin kera na’urorin rarraba wuta da kuma na samar da manyan batira masu amfani da hasken rana.

Farfesa Muhammad Haruna daga bisani ya sanar da cewa a watan Maris na wannan shekarar kuma, hukumar za ta kaddamar da cibiyoyi 24 na bayar da horo kan fasahar kere-kere a sassa daban daban na kasar. (Garba Abdullahi Bagwai)