Ya dace ‘yan siyasar Amurka su saurari ra’ayin kimiyya
2023-01-07 15:38:46 CMG Hausa
Cibiyar yaki da cututtuka masu yaduwa ta kasar Amurka wato IDSA a takaice ta fitar da wata sanarwa jiya Jumma’a, inda ta nuna rashin amincewarta da matakin da Amurka ta dauka, na kayyade masu yawon shakatawa na kasar Sin shiga kasar. Masana cututtuka masu yaduwa da dama sun yi kiraye-kiraye a cikin ‘yan kwanakin da suka gabata cewa, babu bukatar aiwatar da manufar kayyade matafiya daga kasar Sin shiga wasu kasashe. Majalisar kula da filayen tashi da saukar jiragen sama ta kasa da kasa reshen Turai wanda ke wakiltar filayen tashi da saukar jiragen saman nahiyar Turai fiye da 500, ita ma ta soki matakan kayyadewar da aka dauka kan kasar Sin. An ga ainihin yunkurin Amurka shi ne siyasantar da annoba bisa fakewa da kwayar cuta, amma yanzu masana da abin ya shafa suna koya mata ilmin kimiyya.
Amurka tana fama da annoba mai tsanani tun daga watan Disamban bara, alal misali kwayar cutar numfashi da COVID-19 da mura, lamarin da ya sanya tsarin kiwon lafiyarta ya gamu da babbar matsala. A irin wannan yanayi, ba ma kawai gwamnatin kasar Amurka ba ta dauki matakan da suka dace domin dakile matsalolin ba, har ma ta dora laifi kan wasu ta hanyar shafawa kasar Sin bakin fenti.
An lura cewa, yaki da yaduwar annoba yana bukatar ruhin kimiyya, in ba haka ba, za a sha wahala. (Jamila)