logo

HAUSA

Gwamnatin Chadi ta dakile yunkurin kifar da gwamnatin

2023-01-06 21:09:31 CMG HAUSA

 

Gwamnatin kasar Chadi ta ba da sanarwa a jiya Alhamis cewa, jami’an tsaron kasar, sun yi nasarar murkushe wata makarkashiyar hambarar da gwamnatin. Sanarwar ta ce, jami’an soja 11 ne, suka kitsa wannan makarkashiya dake zama barazana ga tsaron kasar.

Gwamnatin Chadi ta ce, an kama wadanda suka aikata laifi, ana kuma gudanar da bincike a kan su. (Amina Xu)