logo

HAUSA

An saka Najeriya cikin jerin kasashen da har yanzu suke bin tsohon tsarin hada-hadar kudade

2023-01-06 10:01:41 CMG HAUSA

 

A ranar 5 ga wata Bankin duniya da Asusun bada lamuni na duniya da kuma kungiyar raya tattalin arzikin kasashen yammacin Afrika Ecowas suka tabbatar cewa Najeriya har yanzu ba ta bin tsarin takaita amfani da takardun kudi a hannun jama’a.

Hukumomin sun ce kudaden da suke yawo a hannun jama’a sun zarta wanda ake da su a banki duk da cewa kasashen duniya sun yi nisa wajen amfani da tsarin cinikayya ta hanyar fasahohi zamani na hada-adar kudade.

Shugaban hukumar dake lura da yadda hukumomi da ma’aikatun gwamnatin Najeriya ke kashe kudaden su Mal. Moddibo Hamman Tukur ya bayyana cikin wata sanarwa a birnin Abuja cewa manyan hukumomin kudade na duniya sun ce hakika Najeriya tana cikin hadari sosai na kalubalen tsaro muddin ba a yi gaggawa takaita amfani da tsabar kudi ba a tsakanin al’umma.

A kan haka ne Mal. Moddibo Hamman Tukur ya ce daga yanzu an haramtawa duk wata hukuma ko ma’aikata ta gwamnati kama daga tarayya, jahohi da kananan hukumomi cirar tsabar kudi daga asusun ajiyarsu na banki kamar yadda ake faruwa a baya, maimakon hakan za su rinka gudanar da duk wata hada hadar kudi ne ta hanyar bankuna ba tare da an debo kudaden a zahiri ba.

Ya ce daga shekara ta 2015 zuwa yau gwamnatin tarayyar Najeriya da gwamnatocin jahohi da na kananan hukumomin kasar su 774 sun ciri tsabar kudi daga bankuna har sama da naira biliyan 500. (Garba Abdullahi Bagwai)