logo

HAUSA

Tattaunawa ita ce hanya daya kacal ta warware batun makamai masu guba na Syria

2023-01-06 20:47:07 CMG Hausa

Wakilin zaunanniyar tawagar kasar Sin a MDD Sun Zhiqiang, ya bayyana cewa, hanya daya tilo ta warware matsalar makamai masu guba a kasar Syria, ita ce tattaunawa da yin shawarwari.

Sun wanda ya bayyana hakan jiya Alhamis, ya ce ya kamata gwamnatin Syria da sakatariyar fasaha ta kungiyar OPCW, ta karfafa cudanya da mu'amala da juna, da ganawa da juna, domin gaggauta daidaita batutuwan da ba a kai ga warwarewa ba. (Ibrahim)