logo

HAUSA

Bai kamata a nuna bambanci kan manufofin kandagarkin COVID-19 da siyasantar da lamarin ba

2023-01-06 21:26:52 CMG HAUSA

 

A yayin taron manema larabai na yau da kullum da ma’aikatar harkokin wajen kasar Sin ta shirya Juma’ar nan. Wani dan jarida ya yi tambaya cewa, kungiyar tarayyar Turai (EU) ta fitar da wata sanarwa a kwanakin baya, inda ta ba da shawara ga mambobinta da su bukaci dukkan fasinjoji daga kasar Sin da su gabatar da takardar sakamakon gwajin kwayar cutar COVID-19 na sa’o’i 48. Ko mene ne ra’ayin kasar Sin kan hakan?

Game da hakan, mai magana da yawun ma’aikatar harkokin wajen kasar Sin Mao Ning ta nuna cewa, Sin ta daidaita manufarta ta kandagarkin COVID-19 bisa alkaluman kimiyya. Kwanan baya, wasu kasashen mambobin EU, sun bayyanawa kasar Sin cewa, suna maraba da masu yawon shakatawa daga kasar Sin sosai, kuma ba za su sanya matakan takaitawa ba. Kwararrun cibiyoyin lafiya irinsu cibiyar kula da cututtuka ta Turai sun bayyana karara cewa, bai dace a sanya takunkumi kan fasinjoji daga kasar Sin ba. Ya kamata EU ta saurari wadannan kiraye-kiraye da idon basira, ta kuma kalli halin da ake ciki game da rigakafin cutar a kasar Sin bisa gaskiya da adalci. (Amina Xu)