logo

HAUSA

Wakilin Sin dake MDD ya yi kira ga Falasdinu da Isra’ila su kai zuciya nesa

2023-01-06 11:56:58 CMG Hausa

Wakilin Sin dake MDD Zhang Jun, ya yi jawabi a taron gaggawa game da batun Falasdinu, wanda kwamitin tsaron MDDr ya gudanar a jiya Alhamis, inda ya yi kira ga bangarorin Falasdinu da Isra’ila da su dakatar da rura wutar rikici tsakaninsu.

Zhang Jun ya ce, wani babban jami’in gwamnatin Isra’ila ya shiga harabar masallacin Aqsa, lamarin ya tsananta yanayin da ake ciki, kuma bangaren Sin ya damu matuka game da hakan.

Kaza lika, bangaren na Sin ya yi kira da a kiyaye, da dawo da zaman lafiya da kwanciyar hankali a wuraren ibada, ya kuma yi kira ga bangarori daban daban da batun ya shafa, da su kwantar da hankali domin kaucewa ta’azzar rikicin.

Ya ce ya dace Isra’ila ta kauracewa dukkan ayyukan tada hankali, ta gujewa dukkanin ayyukan daka iya ingiza mummunan halin da ake ciki. (Safiyah Ma)