logo

HAUSA

Majalissar wakilan Amurka ta dage zaman ta bayan gaza zaben sabon kakaki

2023-01-05 11:35:25 CMG Hausa

Majalissar wakilan Amurka, ta gaza cimma nasarar zaben sabon kakakin ta a zaman ta na daren jiya Laraba, inda daga karshe majalissar ta dage zama zuwa Alhamis din nan.

Rashin zaben sabon kakakin majalissar dai ya tsugunar da harkokin majalissar, duk da cewa, kafin dage zaman na daren jiya Laraba, ‘yan majalissar sun yi ganawar sirri, a kokarin su na warware sabanin da ya haifar da rarrabuwar kawuna.

Yayin zaman na jiya, dan majalissar wakilan California daga jam’iyyar  Republican Kevin McCarthy, ya gaza samu isassun kuri’un da za su ba shi damar darewa mukamin kakakin majalissar sakamakon rarrabuwar kawuna tsakanin ‘yan jam’iyyar sa.

Game da yanayin da ake ciki, shugaban Amurka Joe Biden na jam’iyyar Democrat, ya ce rashin cimma nasarar zaben sabon kakakin majalissar ta wakilai har zuwa yanzu abun kunya ne.

McCarthy dai na da goyon bayan mafiya yawan ‘yan majalissa daga jam’iyyar Republican, da kuma tsohon shugaban kasar Donald Trump, to sai dai kuma akwai wasu ‘yan jam’iyyar sa kalilan da suka ja tunga, suna matukar adawa da zaben sa, tare da bayyana shi a matsayin wanda ba shi da isasshiyar akidar ra’ayin rikau, yayin da ya ki amincewa da sassauta karfin da kujerar kakakin ke da shi.

A wannan karo, daukacin ‘yan jam’iyyar Democrats sun zabi wakilin birnin New York Hakeem Jeffries a matsayin kakakin majalissar, duk da cewa abu ne mai wahalar gaske Jeffries ya cimma nasarar darewa mukamin. Idan kuwa ya yi nasarar hakan, zai kasance dan majalissa na farko dan asalin Afirka da zai jagoranci majalissar dokokin Amurka a tarihin kasar. (Saminu Alhassan)