logo

HAUSA

An gaza fitar da sabon shugaban majalisar wakilai ta kasar Amurka

2023-01-04 13:30:23 CMG Hausa

 

Jiya Talata, aka bude taro karo na 118, na majalisun dajittai da wakilai na kasar Amurka, inda a yayin zaman aka gaza fitar da sabon shugaban majalisar wakilai duk da an kada kuri'a har sau uku.

Shi ne karo na farko da aka gaza zaben sabon shugaban majalissar ta wakilai, bayan gudanar zagayen farko na zabe cikin shekaru fiye da 100 da suka gabata, lamarin da ya sa majalisar wakilan ta shiga uku a siyasance. Hakan ya sa sabbin 'yan majalisar ba za su iya kama aiki yadda ya kamata ba. An ce, majalisar za ta sake gudanar da zaben shugabanta ne a yau Laraba. (Kande Gao)