logo

HAUSA

Shugaban Najeriya ya sanya hannu kan kasafin kudin shekarar 2023

2023-01-04 10:38:55 CMG Hausa

A jiya Talata ne shugaban tarayyar Najeriya Muhammadu Buhari, ya sanya hannu kan kasafin kudi na shekarar 2023, inda ya yi kira ga dukkanin sassa masu ruwa da tsaki da su dukufa wajen aiwatar da shi ba tare da bata lokaci ba, ta yadda hakan zai dace da manufar mika mulki ga zababbiyar gwamnati dake tafe.

Yayin bikin sanya hannu kan kasafin kudin da ya gudana a fadar gwamnati dake birnin Abuja, shugaba Buhari ya ce kasafin na bana, an tsara shi ne ta yadda zai ingiza daidato a fannin kashe kudaden hukuma, da bunkasa hada-hadar manyan sassan tattalin arziki, tare da tabbatar da mika mulki ga sabuwar gwamnatin da ‘yan kasa za su zaba cikin nasara.

Kaza lika a cewar shugaban na Najeriya, an tsara kasafin kudin na 2023 ta yadda zai hade dukkanin sassan raya zamantakewar al’umma, da karfafa juriyar tattalin arzikin kasar.

Kasafin kudin Najeriya na 2023 dai ya kunshi naira tiriliyan 21.83, kimanin dalar Amurka biliyan 48.71, kuma shi ne kasafi na karshe da gwamnatin Buhari za ta fara aiwatarwa, a kasar mafi yawan al’umma a nahiyar Afirka, yayin da ake tunkarar babban zaben watan Fabrairu dake tafe, da kuma mika mulki ga sabuwar gwamnati a watan Mayu. (Saminu Alhassan)