logo

HAUSA

Sin da UAE sun bukaci a kira taron kwamitin sulhu na MDD kan batun masallacin Aqsa

2023-01-04 13:28:38 CMG Hausa

Bisa labarin da wakilin CMG ya samu, an ce, a jiya Talata, Sin da hadaddiyar daular Larabawa ta UAE, sun bukaci kwamitin sulhun Majalisar Dinkin Duniya ya kira taron gaggawa a kwanakin dake tafe, don tattaunawa kan halin da masallacin Aqsa yake ciki, wanda yake a yankin babban wurin ibadar Yahudawa na Temple Mount dake birnin Kudus. An ce, ana sa ran za a kira taron a ranar Alhamis 5 ga watan nan.

A safiyar ranar 3 ga wata bisa agogon wurin, Itamar Ben-Gvir, shugaban Jam’iyyar Otzma Yehudit mai matukar tsattsauran ra’ayi na kasar Isra’ila, kana ministan kwantar da kura na kasar ya ziyarci Temple Mount dake tsohon birnin Kudus, matakin da sassan Palesdinu suka yi matukar suka. (Kande Gao)