logo

HAUSA

Iran ta yi maraba da dukkan matakai masu inganci dake taimakawa kyautata dangantakar tsakanin ta da Masar

2023-01-03 13:31:33 CMG Hausa

Kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar Iran Nasser Kanaani, ya bayyana a jiya Litinin cewa, Iran tana maraba da dukkan matakai masu inganci, dake taimakawa kyautata dangantakar tsakaninta da Masar.

A yayin taron ‘yan jarida na mako mako da aka gudanar a ran nan, Kanaani ya bayyana cewa, yayin da ya hallarci taron bunkasa dangantakar abokantaka da hadin gwiwa na Baghdad karo na biyu a birnin Amman, wato babban birnin kasar Jordan a watan da ya gabata, ministan wajen Iran Abullahi ya zanta da shugaban Masar Abdel Fattah al Sisi, da ministan wajen Masar Sameh Hassan Shoukry. Bangarorin biyu sun yarda da gudanar da tattaunawa, da kuma cimma manufofin warware matsalolin jakadanci na kasashen biyu.

An gudanar da juyin juya halin Musulunci a kasar Iran a shekarar 1979, lamarin da ya kawo karshen daular Pahlavi. Kuma a shekarar ne Masar da Isra’ila suka sa hannu kan yarjejeniyar zaman lafiya, tare da ba da mafakar siyasa ga shugaban Iran mai gudun hijira, kana daga bisani Iran ta sanar da katse dangantakar diplomasiyya tsakaninta da Masar. Kuma har yanzu kasashen biyu ba su mayar da dangantakar jakadanci ba.(Safiyah Ma)