logo

HAUSA

Kasashen dake kewayen tekun Pacific suna da ’yancin neman diyya daga Japan

2023-01-03 21:10:08 CMG HAUSA

 

Shahararrun ‘yan siyasa na kasar Vanuatu sun yi shelar cewa, idan ruwan dagwalon nukiliya ba shi da wata matsala, to a zubar da shi a Tokyo, idan kuma an bincika a Paris to a ajiye shi a Washington, amma a yi nesa da yankin tekun Pacific da nukiliya. Wannan ita ce daukacin ra’ayin jama’a a wannan yankin.

A watan Afrilu na shekarar 2021 ne, gwamnatin Japan ta sanar da zubar da ruwan dagwalon nukilya a cikin tekun Pacific daga bazarar shekarar 2023. Yayin da wannan lokaci ke karatuwa, ‘yan a’dawa na sassan duniya na nuna rashin jin dadi kan wannan lamari. A yankin tekun Pacific, jama’a na kokawa matuka game da shirin Japan na zubar da ruwan dagwalon nukiliyar a cikin teku. Manazarta na bayyana cewa, idan Japan a gaske take kan wannan batu, to kasashen dake kewayen tekun ma suna da ‘yancin neman diyya daga gare ta. (Amina Xu)