logo

HAUSA

Ministan wajen Sin ya tattauna da takwaransa na Amurka ta wayar tarho

2023-01-02 15:38:26 CMG Hausa

Jiya Lahadi 1 ga wata ne, ministan harkokin wajen kasar Sin kuma jakadan kasar dake kasar Amurka Qin Gang ya tattauna da sakataren harkokin wajen kasar Amurka Antony Blinken ta wayar tarho, inda Qin Gang ya yi ban kwana da Blinken, tare kuma da waiwaye kan ganawar da suka yi, yayin da yake rike da mukamin jakadan Sin dake Amurka. Kana yana fatan zai ci gaba da kiyaye huldar aiki mai kyau dake tsakaninsu, ta yadda za a ingiza kyautatuwa da ci gaban huldar dake tsakanin Sin da Amurka.

Haka zalika sassan biyu sun isar da gaisuwar sabuwar shekara ga juna. (Jamila)