logo

HAUSA

’Yan kasuwar jamhuriyar Nijar na fatan kasuwancin da ake yi tsakanin Sin da Nijar zai samu ci gaba a shekara ta 2023

2023-01-01 17:45:12 CMG HAUSA

 

Rahoto farfadowar kasuwanci da tattalin arziki a Nijar ta dalilin ’yan kasuwar jamhuriyyar kasar dake yin odar kayayyaki daga kasar China, duk da matakan kandagarkin yaki da cutar covid-19 da ake dauka suna janyo tafiyar hawainiya ga tattalin arzikin duniya, sai dai kasashen Afrika, kamar misalin kasar Nijar sun fara ganin sa ida ta fuskar ci gaban kasuwanci tun lokacin da hukumomin China suka sassauta shigo da kaya daga kasar Sin. Ga rahoton da wakilinmu Mamane Ada ya hada mana daga Yamai.//////

Kamar sauran kasashen duniya, matakan rigakafi domin dakile annobar covid 19 sun janyo illoli sosai ga ci gaban tattalin arzikin kasashen Afrika, musamman ma tattalin arzikin Nijar da ya yi fama da karancin abubuwan more rayuwa dake fitowa daga kasar China. Sai dai ’yan kasuwa a Nijar na ganin cewa, duk da wannan matsala, dangantaka tsakanin Afrika da China za ta taimakawa bunkasuwar tattalin arziki da jorewa matsalolin kasuwanci a nan gaba, ta yadda hada hada za ta dore ga yawancin ’yan kasuwa na Nijar dake sayen kaya daga China.

Alhaji Halla Mahamadu, shugaban kungiyar ’yan kasuwa a birnin Tahoua, ya bayyana cewa:

Dangantakarmu da China tana da karfi tun da ban da Tahoua ma, Nijar gaba daya mutane suna zuwa China sosai. Visa na China, gaskiya yana da saukin samu, kuma zuwan kayayyaki kuma babu wata matsala. Kome da ka sani mutane suna kawo su daga China kamar tufafi, kayayyakin gini da takalma duka, sai in ce kusan kowane irin kalar kaya gaskiya ana sayensu daga China. Kayansu gaskiya suna da kyau, muna nan idan ka duba nan gare mu Afrika, mutane za ka gani mafi galibi gaskiya sauki ne suke so.

Alhaji Abdul Nasser Addu, dan kasuwa da ya kwashe shekaru yana zuwa China wajen sayen kaya dake zaune a birnin Tahoua ya bayyana cewa, zuwa kasar China ya yi wuya, tun bayan daukar matakan kandagarki domin hana yaduwar cutar lumfashi ta Covid-19 da gwamnatin China ta dauka, wanda a lokacinsa shiga kasar ya yi matukar wuya ga ’yan kasuwa. Ya yaba da yadda kasar China take taimakawa ci gaban tattalin arzikin nahiyar Afrika musamman ma tare da jamhuriyyar Nijar.

« Ai idan ka duba ka gani ma akasarin kayan duniya ma, to ka dauka daga tarayyar Turai har zuwa kasar Amurka duk kayayyakin kirar kasar China ne suke aiki da su, domin akwai riba, saboda gaskiya China tana saukaka ma ’yan kasuwa dake sayen kaya, wannan shi ne riba, ke nan kayan China gaskiya idan dai akwai kayan China to akwai wuya sauran kayayyakin kasashe su samu shiga. »

A nasa bangare, Alhaji Salisu Abdullahi, babban manajan kamfanin sarrafa katifu na Ihsane Foam dake birnin Yamai, ya yi kira ga shugabannin kamfanonin kasar China da su yi kokarin kafa cibiyoyin masana’antunsu a Nijar domin kawo sauki ga ’yan kasuwar Nijar. Yana mai cewa :

« Matsalolin da muke cin karo da su su ne kamfanonin da muke aiki da su ko kuma irin kayan da muke aiki da su, kamfanonin ba su da cibiyoyi a nan, ba su da wannan wakilta a nan, ya kamata a ce suna da reshe wanda idan za mu odar kaya sai mu je reshensu, amma ba wai sai mun je China ba, idan akwai wannan sai mu je wajen reshensu sai mu fada musu abin da muke so, mu yi odar kaya daga wajensu, su fada mana kasonsu da suke so, mu ba su kasonsu. Idan kayanmu suka zo tashar ruwan Cotonou sai mu cika musu sauran cikon kudinsu. To idan wadannan kamfanoni na China suka zo suka kafa rassansu a nan kasarmu ta Nijar, idan aka yi haka wahala za ta rage. Kuma wajen yin oda za a samu sauki sosai. Idan za ka oda daga China, kowane kaya kake so su za ka je ka gani a nan Nijar, suna da wakilansu wanda hankalinka zai kwanta ba za ka fada hannun ’yan danfara ba. « 

Tuni dai hukumomin kasar China suka fara daukar matakan sassauta wannan matsala, domin taimakawa farfado da tattalin arzikin kasashen Afrika, kamar su Nijar.

Daga birnin Niamey  na jamhuriyyar Nijar, Maman Ada, sashen hausa na CRI.