logo

HAUSA

Jawabin shugaban kasar Sin a sabon shekara wata kyauta mai kyau ga duniya

2023-01-01 17:20:13 CMG HAUSA

 

Yau ranar farko ta shekarar 2023, al’ummar duniya na maraba da hasken rana a sabuwar shekara don bayyana fatansu na samun zaman lafiya da bunkasuwa.

Shugaban kasar Sin Xi Jinping ya ba da jawabi a jiya, inda ya nanata hulda ta kut da kut tsakaninta da duniya, kuma Sin za ta ci gaba da samun bunkasuwa nan gaba, kuma yana mai fatan za a samun zaman lafiya da kwanciyar hankali da alheri nan gaba.

Duniya da Sin na amfanawa juna ne, ra’ayin JKS mai mulkin Sin ke da shi. A cikin shekara daya da ta gabata, bunkasuwar Sin na bayyana cewa, Sin mai kokarin cimma muradunta da cike da kuzari dake da ruhin hadin kai tsakanin kabilu da mai da hankali matuka kan huldar dake tsakaninta da duniya, bunkasuwarta ba ma kawai ya kawo amfani a cikin kasa ba, har ma za ta amfanawa duk fadin duniya baki daya. (Amina Xu)