logo

HAUSA

Yadda biranen Sin suka farfado yana aike kyakkyawan sako ga duniya

2023-01-01 20:21:08 CMG Hausa

Tun bayan da kasar Sin ta daidaita matakanta na yaki da annobar COVID-19, titunan birnin Beijing sun sake cunkushewa, masu yawon bude ido suna tururuwa don zuwa hutu a kasashen waje, yayin da 'yan kasuwa suke sa ran farfadowar harkokin kasuwanci, mutane suna jira a layi a yayin harkokin karshen mako a cibiyar shakatawa ta Shanghai Disneyland da wurin shakatawa na Universal dake birnin Beijing, zirga-zirga a otel-otel dake wuraren shakatawa shi ma ya karu matuka, yadda jama’a ke tururuwa cibiyar kasuwanci ta Beijing ya farfado sosai, kana tsarin kiwon lafiya na Beijing yana gab da dacewa da yanayin da ake ciki.

Wannan shi ne sabbin abubuwa da Financial Times, Reuters da kamfanin dillancin labarai na Eiffe suka lura da su a kasar Sin.

An gano cewa, rayuwar jama'ar kasar Sin na komawa kamar yadda aka saba a baya, yanayin kasuwanci a titunan biranen Beijing da Shanghai yana kyautatuwa, su ne suka mamaye muhimman shafukan kafofin watsa labaru na kasashen waje da dama. (Ibrahim)