logo

HAUSA

’Yan Najeriya na murna bankwana da 2022 wadda ta kasance cike da kalubalen tattalin arziki da na tsaro

2023-01-01 15:50:26 CMG HAUSA

 

Yau 1 ga watan Janairun 2023 ’yan Najeriya sun shafe daren Lahadi suna addu’o’i tare da shagulgulan ban kwana da shekara ta 2022.

Kusan dukkan al’umomin dake shiyyoyi shida na kasar sun fito rukuni-rukuni suna murna ba kamar yadda ya faru a ’yan shekaru biyu da suka gabata ba sakamakon annobar Covid-19 wanda a wancan lokaci suka gaza samu sakewar haduwa wuri guda domin nuna murnar shiga sabuwar shekara.

Koda yake dai a wasu jahohin musamman wadanda ke arewacin Najeriya jami’an tsaro sun haramta a shagalin sabuwar shekarar kamar yadda aka saba saboda yanayi na tsaro.

A sakon sabuwar shekara na karshe a kan gadon mulki shugaban kasa Muhammadu Buhari ya tabbatarwa ’yan kasar kudurinsa na gudanar da sahihin zabe wanda kowa zai gamsu da shi .

Shugaba Buhari ya yi kira ga dukkan ’yan Najeriya da su sanya kyakkyawan fata a sabuwar shekara ta 2023 cikin  zuciyarsu, tare da kara jajircewa wajen hidimtawa kasa.

Ya ci gaba da cewa hakika ya fuskanci suka da dama daga ’yan Najeriya a shekarar da muka yi ban kwana da ita, amma ya san cewa ya yi bakin kokarinsa kuma yana da yakinin cewa magajinsa zai dora domin tabbatar da cikar burin ganin Najeriya ta kasance daya daga cikin kasashe mafiya daukaka a duniya a wannan sabuwar shekara. (Garba Abdullahi Bagwai)