logo

HAUSA

Manyan jami’an JKS sun mika rahoton ayyukansu ga kwamitin tsakiya na Jam’iyyar

2022-02-28 14:30:04 CRI

Manyan jami’an JKS sun mika rahoton ayyukansu ga kwamitin tsakiya na JKS da kuma Xi Jinping, Sakatare Janar na kwamitin tsakiyar.

Jami’an, mambobi ne na ofishin siyasa da na sakatariyar kwamitin tsakiyar JKS da mambobin rukunonin jagororin jam’iyyar na kwamitin dindin din na majalisar wakilan jama’ar kasar da na majalisar gudanarwar kasar da na majalisar tuntuba kan harkokin siyasa da kuma sakatarorin rukunonin jagororin jam’iyya na kotun koli kasar da kuma hukumar koli mai kula da karrakin jama’a.

Bayan nazartar rahoton ayyukan, Xi Jinping ya bukaci su da shiryawa babban taron wakilan jam’iyyar karo na 20 da za a yi a karshen shekarar da muke ciki, tare da kwararan matakai. (Fa’iza Mustapha)