logo

HAUSA

Jihar Xinjiang ta tura lantarkin da ya haura kWh biliyan 500 ga sauran sassan kasar Sin

2022-02-28 13:38:57 CRI

Jihar Xinjiang ta tura lantarkin da ya haura kWh biliyan 500 ga sauran sassan kasar Sin_fororder_220228-Xinjiang-Faeza3

Tun daga shekarar 2010 zuwa yanzu, jihar Xinjiang ta Uygur mai cin gashin kanta dake arewa maso yammacin kasar Sin, ta tura jimilar lantarki da ya kai kWh biliyan 503.7 ga sauran sassan kasar Sin.

Cibiyar turakun lantarki ta jihar ta ce, daga cikin adadin, an samar da kWh biliyan 137.8 daga makamashin da ake iya sabuntawa wato hasken rana da karfin iska. Wanda ya yi daidai da kona ton miliyan 41 na kwal, lamarin da ya rage fitar da sinadarin carbon dioxide da ton miliyan 110, tare da bada gagarumar gudunmawa ga shirin kasar na rage fitar da hayaki mai guba.

Cikin shekaru 11 da suka gabata, cibiyar ta gina hanyoyi 4 na tura makamashi a Xinjiang, domin tura lantarkin da aka samar a yankin zuwa wasu sassan kasar Sin 20 dake matakin lardi.

Jihar Xinjiang na da arzikin albarkatun makamashi, ciki har da na iska da hasken rana, wadanda ke bunkasa karfin samar da makamashi. Da wadancan hanyoyin tura makamashi da aka gina, jihar na iya turawa da sayar da makamashi ga sauran sassan kasar Sin. (Fa’iza Mustapha)