logo

HAUSA

Sojojin Somaliya sun kashe mayakan al-Shabab 5

2022-02-28 11:34:03 CRI

Sojojin Somaliya sun kashe mayakan al-Shabab 5_fororder_220228-Somali-Ahmad3

Rundunar sojojin kasar Somaliya (SNA), ta sanar a ranar Lahadi cewa, dakarunta sun kashe mayakan ’yan ta’addan kungiyar al-Shabab biyar, a lokacin wani farmaki da suka kaddamar a yankuna masu makwabtaka da gundumar Balad, da Afgoye, dake arewa maso gabashi da kudu maso yammacin birnin Mogadishu.

Kwamandan rundunar SNA, wanda ya jagoranci ayyukan farmakin, ya shedwa gidan radiyon Mogadishu cewa, sun yi nasarar lalata maboyar mayakan ’yan ta’addan da dama dake cikin wasu gonaki, a lokacin da suka kai farmakin.

Dakarun gwamnatin Somaliya sun zafafa hare-haren da suke kai wa kan mayakan kungiyar ta al-Shabab, a tsakiya, da kuma shiyyar kudancin kasar a baya bayan nan, sai dai har yanzu, mayakan ’yan ta’addan su ne ke iko da manyan kauyuka da dama dake wadannan shiyyoyi, inda suke ci gaba da kai hare haren kwanton bauna da kuma daddasa boma-boman karkashin kasa. (Ahmad)