logo

HAUSA

Iran ta bukaci kasashen yamma su yanke shawara game da tattaunawar Vienna

2022-02-28 10:21:48 CRI

Iran ta bukaci kasashen yamma su yanke shawara game da tattaunawar Vienna_fororder_220228-Iran-Faeza1

Ma’aikatar harkokin wajen Iran, ta bukaci kasashen yamma dake cikin tattaunawar da ake yi a Vienna, su yanke shawara a siyasance, domin warware takkadama game da yarjejeniyar nukiliya ta 2015.

Kakakin ma’aikatar Saeed Khatibzadeh, ya shaidawa kamfanin dillancin labarai na kasar IRNA cewa, tattaunawar ta Vienna ta kai wata gaba dake bukatar matakan siyasa masu karfi daga Amurka da kasashen Yamma.

Ya ce ya kamata wadannan matakai su mayar da hankaIi kan dage takunkuman da Amurka ta kakabawa Iran da kuma bada tabbaci dangane da su.

Ya kara da cewa, idan daya bangaren ya girmama bukatun Iran tare da daukar matakai a siyasance, ya tabbata cewa Iran, za ta kammala yarjejeniyar nan ba da jimawa ba.

Bugu da kari, Iran ba za ta amince da sanya mata wa’adin cimma yarjejeniya ba, yana mai kira ga hukumar kula da makamashin nukiliya ta duniya, ta kawo karshen zarge-zargen da ake wa kasar. (Fa’iza Mustapha)