logo

HAUSA

Najeriya ta fidda sabuwar ranar zaben shugaban kasa na shekarar 2023

2022-02-27 15:28:09 CRI

Hukumar zaben Najeriya ta ayyana ranar 25 ga watan Fabrairun shekarar 2023, a matsayin ranar zaben shugaban kasar, inda aka samu karin mako guda a bisa ranar da aka tsara don gudanar da zaben tun da farko.

Shugaban hukumar zabe mai zaman kanta ta kasar INEC, Mahmood Yakubu, ya ce za a gudanar da zaben ‘yan majalisar dokokin tarayyar kasar a rana guda da na shugaban kasar.

Hukumar ta INEC ta sanar da ‘yan jaridu a Abuja, babban birnin kasar cewa, zaben gwamnoni, da na ‘yan majalisun dokokin jahohin kasar za su gudana ne a ranar 11 ga watan Maris na shekarar 2023, wato an samu karin mako guda a bisa ranar farko da aka sanya don gudanar da zaben wato ranar 4 ga watan Maris.

A ranar Juma’ar da ta gabata, shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya sanya hannu kan dokar zaben kasar da aka yi wa kwaskwarima, gabanin gudanar da manyan zabukan shekara mai zuwa a kasar mafi yawan al’umma a Afrika.

A lokacin kwarya-kwaryar bikin sanya hannu kan dokar zaben, wanda aka gudanar a fadar shugaban Najeriya dake Abuja, shugaba Buhari ya ce, aikin gyaran dokar zaben zai taimaka matuka wajen tabbatar da ingancin zabuka a Najeriya, yayin da aka bullo da tsarin amfani da sabbin fasahohin zamani, a kokarin tabbatar da sahihancin zabe a kasar.(Ahmad)

Ahmad