logo

HAUSA

Sin ta bukaci Amurka ta mayarwa Afghanistan dukiyarta

2022-02-26 17:24:50 CRI

Sin ta bukaci Amurka ta mayarwa Afghanistan dukiyarta_fororder_5bafa40f4bfbfbedde544d13286a173faec31ff4

Ma’aikatar harkokin wajen kasar Sin ta bukaci kasar Amurka ta mayarwa kasar Afghanistan dukiyar al’ummar kasar, ba tare da gindaya wasu sharruda ba, kana ta dauki kwararan matakan gyara irin barnar da ta haifar musu.

Global Times, wata jaridar Turanci ta kasar Sin, ta shigar da korafi ta kafar intanet a ranar Alhamis, inda ta nemi gwamnatin kasar Amurka da ta mayar da kudaden don ceto rayukan al’ummar kasar Afghanistan.

Da aka bukaci ya yi tsokaci game da batun korafin, kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar Sin, Wang Wenbin, ya bayyanawa taron manema labarai cewa, korafin da aka gabatar ya samu amincewar masu bibiyar shafin intanet sama da 200,000 cikin sa’o’i 24. Yace wannan ya nuna cewa, abin da Amurka ta yiwa kasar Afghanistan tamkar fashi ne, kuma ya fusata jama’a.(Ahmad)