logo

HAUSA

Kauyukan wasannin Olympics na nakasassu na lokacin hunturu dake Beijing, Yanqing, Zhangjiakou sun bude a hukunce

2022-02-26 17:31:56 cri

Kauyukan wasannin Olympics na nakasassu na lokacin hunturu dake Beijing, Yanqing, Zhangjiakou sun bude a hukunce_fororder_下载

Za a bude wasannin Olympics na nakasassu na lokacin hunturu na Beiijing na shekarar 2022 a ranar 4 ga wata mai kamawa. A jiya Jumma’a, aka bude kauyukan wasannin Olimpics na nakasassu na lokacin hunturu dake Beijing, Yanqing da kuma Zhangjiakou a hukunce. An mayar da kauyukan ne daga kauyukan wasannin Olympics na lokacin hunturu, wadanda za su karbi tawagogi guda 48.

Andrew Parsons, shugaban kwamitin wasannin Olimpics na nakasassu na kasa da kasa, ya bayyana cewa, yana sa ran ganin an gudanar da wasannin nakasassu na lokacin hunturu na Beijing yadda ya kamata.

A cewarsa, kasar Sin da kwamitin shirya gasar wasannin Olympics na nakasassu na lokacin sanyi na birnin Beijing sun yi kokari sosai domin samar da yanayi mai inganci a gasar, don haka 'yan wasa na bukatar su maida hankali kan gasar, da yin gasar bisa tsari mafi dacewa, da kuma jin dadin gudanar da gasar cikin yanayi mai kyau. (Bilkisu Xin)