logo

HAUSA

Wang Yi ya bayyana matsayin kasar Sin a fannoni 5 kan batun Ukraine

2022-02-26 17:10:30 cri

Wang Yi ya bayyana matsayin kasar Sin a fannoni 5 kan batun Ukraine_fororder_src=http___wx3.sinaimg.cn_crop.0.0.1339.745_006KQV1Aly1gzqq53gb1oj31180le773&refer=http___wx3.sinaimg

Jiya Jumma’a, mamban majalisar gudanarwar kasar Sin, kuma ministan harkokin wajen kasar Wang Yi, ya zanta ta wayar tarho da sakatariyar harkokin wajen kasar Birtaniya Liz Truss, da babban wakilin kungiyar EU mai kula da harkokin waje da manufofin tsaro Josef Borell, da mai ba da shawara ga shugaban kasar Faransa, Emmanuel Bonne, inda suka maida hankali kan musayar ra'ayi game da halin da ake ciki a Ukraine.

Game da matsayin da kasar Sin ke dauka kan batun Ukraine, Wang Yi, ya bayyana wasu fannoni biyar.

Na farko, kasar Sin tana tsayawa kan mutunta mulkin kan kasa, da cikakken yankin kasa na kasashe daban daban, da kiyaye manufofi, da ka'idojin kundin tsarin mulkin MDD. Wannan shine matsayin da take bi a koda yaushe, wanda kuma ke dacewa da batun Ukraine.

Na biyu, kasar Sin na ba da shawarar bin ra'ayin tsaro na bai daya, da cikakken hadin kai mai dorewa. A ganinta, bai kamata a tabbatar da tsaron wata kasa ta hanyar tauye tsaron wasu kasashe ba, kuma ba za a iya tabbatar da tsaron yankin ta hanyar karfafa ko fadada kungiyoyin soja ba.

Na uku, kasar Sin tana mayar da hankali kan sauyin yanayin da Ukraine ke ciki, halin da kasar ke ciki yanzu wani abu ne da bamu so ganin haka.

Na hudu, kasar Sin tana goyon baya da karfafa duk wani yunkurin diflomasiyya da zai taimaka wajen warware rikicin Ukraine cikin lumana. Kasar Sin tana maraba da yin shawarwari kai tsaye tsakanin Rasha da Ukraine cikin sauri.

Na biyar, kasar Sin na ganin cewa, ya kamata kwamitin sulhu na MDD ya taka muhimmiyar rawa wajen warware batun Ukraine. Kuma kamata ya yi matakan da kwamitin zai dauka su kasance na kwantar da hankulla, amma ba na rura wutar rikicin ba. (Mai fassara: Bilkisu Xin)