logo

HAUSA

Rasha tana cigaba da rusa gine-ginen soja na Ukraine yayin da ake fatan bangarorin zasu tattauna

2022-02-26 17:45:53 CRI

图片默认标题_fororder_VCG111370936517

Kasar Rasha tana cigaba da yin matsin lamba kan Ukraine, ta hanyar kaddamar da karin hare-hare kan gine-ginen sojoji a kasar Ukraine, yayin da bangarorin biyu suka bayyana aniyarsu na fara tattaunawar sulhu.

Kakakin ma’aikatar tsaron Rasha, Igor Konashenkov, ya bayyana a daren Juma’a cewa, dakarun sojojin kasar Rasha sun lalata gine-ginen sojoji 211 a Ukraine tun bayan kaddamar da hare-haren da safiyar Alhamis.

Konashenkov yace, a lokacin yakin, sojojin Rashar sun kwace makaman yaki masu yawan gaske wanda kasashen yammacin duniya suka aikawa Ukraine, tun a wasu watanni da suka gabata.

Sojojin Rasha sun yiwa birnin Kiev kawanya, bayan sun kwace iko da filin jirgin saman Gostomel dake birnin Kiev, inda suka kashe dakarun rundunar yaki ta musamman ta Ukraine sama da 200.

Kakakin ma'aikatar harkokin wajen Rasha Sergei Lavrov, ya bayyanawa taron manema labarai cewa, Rasha bata da niyyar mamaye Ukraine, kuma gwamnatin Moscow, a shirye take ta tattauna kai tsaye, idan har dakarun kasar Ukraine sun amince su kwance damarar yakinsu.

Bugu da kari a ranar Juma'a, shugaban kasar Ukraine, Volodymyr Zelensky, ya gabatar da jawabi kai tsaye ga 'yan kasar, inda ya bayyana cewa, yana son tattaunawa da Rasha.

A halin yanzu, Ukraine da Rasha suna tattaunawa game da lokaci da kuma wajen da za su shirya tattaunawar sulhu, yayin da tattaunawar zata gudana nan bada jimawa ba, akwai sauran damammaki na tabbatar da ganin al'amurran rayuwar yau da kullum sun dawo kamar yadda aka saba, a cewar sakataren yada labaran Zelensky, Serhiy Nikiforov.(Ahmad)

CRI