logo

HAUSA

Xi ya jaddada aniyar Sin ta dagewa kan batun bunkasa hakkin dan adam

2022-02-26 16:52:03 CRI

Xi ya jaddada aniyar Sin ta dagewa kan batun bunkasa hakkin dan adam_fororder_微信图片_20220226165132

Babban sakataren kwamitin kolin jam’iyyar kwaminis ta kasar Sin (CPC),  Xi Jinping, ya jaddada aniyar kasarsa na nacewa kan tafarkin ayyukan dake shafar bunkasa hakkin dan adam.

Xi, yayi wannan tsokaci ne a lokacin da ya jagoranci wani taron hukumar siyasa ta kwamitin kolin jam’iyyar CPC a ranar Juma’a.

Shugaba Xi, ya kuma yi kiran a kara himma, wajen mayar da hankali, kan batutuwan dake shafar mutuntawa da kiyaye hakkokin bil adama, da kuma kara daga matsayin ayyukan kare hakkin dan adam na kasar Sin, yayin da kasar ta dukufa wajen gina kasa mai tsarin gurguzu na zamani daga dukkan fannoni.(Ahmad)