logo

HAUSA

Wang Yi ya halarci muhimmin taro game da rigakafin COVID-19 na babban taron MDD

2022-02-26 20:50:19 cri

Wang Yi ya halarci muhimmin taro game da rigakafin COVID-19 na babban taron MDD_fororder_src=http___bbs.fmprc.gov.cn_web_wjbzhd_202202_W020220226292638996734&refer=http___bbs.fmprc.gov

Jiya Jumma’a, mamban majalisar gudanarwar kasar Sin, kana ministan harkokin wajen kasar Wang Yi, ya halarci muhimmin taro game da alluran rigakafin COVID-19 na babban taron Majalisar Dinkin Duniya ta kafar bidiyo.

Wang Yi ya ce, ana kara samun yaduwar annobar COVID-19 a cikin shekaru biyun da suka gaba. Sai dai a bisa kokarin hadin gwiwar da kasashen duniya ke yi tare, an samu babban ci gaba wajen yin alluran rigakafin a duniya, amma har yanzu ana fuskantar matsalar rashin daidaito wajen rarraba alluran rigakafin. Game da haka, kasar Sin ta gabatar da shawarwari guda hudu.

Na farko, tace kamata ya yi a karfafa “tsarin tsaro” na rigakafin cutar, da dora muhimmanci kan marawa kasashe masu tasowa baya, musamman ma kasashen Afirka. Na biyu, ya kamata a kara yawan matakan yaki da annobar, da kara kyautata matakan rigakafi da shawo kan cutar, kana a karfafa hadin kai wajen yin nazari game da yadda cutar ke sauya kamanninta da samar da magunguna dakile tasirin cutar ta hanyar kara yin alluran rigakafin. Na uku, ya kamata a kara kyautata yanayin kiwon lafiya, da ba da taimako na hakika ga kasashe masu tasowa wajen karfafa tsarin kiwon lafiyarsu. Na hudu, a ba da tabbaci wajen samun ci gaba, a yayin da ake kokarin shawo kan annobar, ya kamata a mayar da hankali kan neman bunkasuwar tattalin arzikin kasashen duniya. (Mai fassara: Bilkisu Xin)