logo

HAUSA

Kwamitin sulhun MDD bai zartas da daftarin kuduri kan halin da ake ciki a Ukraine ba

2022-02-26 17:12:07 cri

Kwamitin sulhun MDD bai zartas da daftarin kuduri kan halin da ake ciki a Ukraine ba_fororder_1128418607_16458442560221n

Jiya Jumma’a, Kwamitin Sulhu na Majalisar Dinkin Duniya ya kada kuri'a kan daftarin kudurin da kasashen Amurka da Albaniya suka gabatar kan halin da ake ciki a Ukraine. Daftarin kudurin ya gaza samun amincewa saboda watsin da Rasha tayi da kudirin. Kasar Sin ta kada kuri’ar janye jiki.

Wakilin din din din na kasar Sin dake MDD Zhang Jun, ya ba da jawabi bayan kada kuri’ar, inda ya bayyana cewa, Kwamitin Sulhun ya gudanar da tarukan gaggawa sau biyu a cikin makon da ya gabata, kuma dukkanin bangarorin sun bayyana cikakken matsayi da damuwarsu kan halin da ake ciki. Duba da halin da ake ciki mai sarkakkiya, ya kamata kwamitin sulhu ya gabatar da martanin da ya dace, a sa’i guda kuma, ya yi taka tsantsan kwarai da gaske. Dole ne duk wani matakin da za a dauka ya taimaka da gaske wajen kwantar da tarzoma, amma ba hura wutar rikici ba. Idan ba a dauki matakai masu dacewa ba, kuma matsa lamba da saka takunkumi, babu abinda zai haifar sai karin hasarar rayuka, da hasarar dukiya, da kara haifar da rudani, da wahalhalu wajen kawar da bambance-bambance, tare da rufe kofar sulhu ta hakika, sannan kuma a karshe wadanda zasu gamu da babbar hasara su ne fararen hula. Bisa wadannan abubuwan da aka ambata a gaba, kasar Sin ta kaurace wa kada kuri'a kan daftarin kudurin. (Bilkisu Xin)