logo

HAUSA

Shugaban Ukraine ya yi kira ga Rasha da fara tattaunawa kan dakatar da ayyukan soji

2022-02-25 20:35:57 cri

Shugaban Ukraine ya yi kira ga Rasha da fara tattaunawa kan dakatar da ayyukan soji_fororder_c9fcc3cec3fdfc033ba71756a533769da5c22613

Bangaren Ukraine ya fada a yau Jumma’a cewa, sojojin kasar Rasha na ci gaba da kutsawa cikin sauri zuwa tsakiyar birnin Kiev, fadar mulkin Ukraine. Shugaban kasar ta Ukraine Volodymyr Zelensky, ya yi kira ga Rasha, da ta soma tattaunawa kan dakatar da ayyukan soji.

Zelensky ya gabatar da wani jawabi ta kafar bidiyo da sanyin safiyar yau, inda ya ce, Ukraine na yaki ita kadai, kuma kawo yanzu mutane 137 sun rasu, yayin da wasu 316 suka jikkata a bangaren Ukraine.

Zelensky ya zargi Amurka da kasashen yammacin duniya da rashin bayar da hakikanin goyon baya ga Ukraine, maimakon hakan an kyale sojojin Ukraine na yaki su kadai, kuma babu wata kasa da ta ba wa Ukraine tabbacin tura sojoji.

A dai wannan rana, shi ma mai ba da shawara ga ofishin shugaban kasar Ukraine, ya wallafa a shafin sada zumunta cewa, bayan kazamin fada da aka gwabza, an kwace ikon mallakar tashar nukiliya ta Chernobyl daga dakarun Ukraine, wadda a yanzu haka sojojin Rasha suka mamaye ta. (Bilkisu Xin)